Sei sulla pagina 1di 4

TABBATACCE KUMA INGANTACCEN TARIHIN IZALA DAGA IBRAHIM UMAR JOS.

Mu da muka saka hannu a kasa, mu ne executive council members na jama'atu izalatil bid'a
wanda aka zaba na tsawon shekara daya, wanda lokacin ya fara daga 8th february 1978 zuwa
7th february 1979 saboda aiwatar da babi na 3 na constitution din mu.

Mu da muka saka hannu a kasa, wakilai ne masu ikon gudanarwa karkarkashin executive
secretary na wannan kungiyar musulunci saboda fitar da constitution don yadawa duniya.

1. Alhaji sale ahmadu (chairman)

2. Alhaji yunusa abdullahi (vice chairman)

3. Alhaji yaya agha abubakar (executive seccretary)

4. Alhaji muhammad tanimu (general secretary)

5. Alhaji tsoho mai magani (finance secretary)

6. Alhaji ibrahim chidawa (treasurer general)

7. Alhaji garba mohammed (publicity secretary)

8. Alhaji m. namaska (complaints secretary)

9. Alhaji adamu hussain (committee executive).

Hoto: mal. Samaila idris da col. Alhassan.

chairman da mataimakin sa ne kawai suka rasu. sauran duk suna raye suna kuma cikin garin
jos.

TSARIN DOKOKIN KUNGIYAR MUSULUNCI NA JAMA'ATU IZALATIL BIDI'A. RANAR


8/3/1978.

Wannan shine kundin tsarin dokokin kungiyar nan ta muslunci, da za'a santa a kuma kira ta da
suna "JAMA'ATU IZALATIL BIDI'A".

Duk abinda aka tsara acikinsa, kaddararta ne kuma kayanta ne, ita daya, batayi tarayyaba da
kowa, wajan mallakarsa.

1. A sani cewar dukkan sassan wannan dokoki, ana iya sake su ko dai dai shekara, ko lokaci,
lokaci, in har kwamitin zartaswar wannan kungiyar taga yin hakan shi yafi dacewa da ayi.
2. kuma a sani cewar shirye muke da mu dinga buga jaridar nan da ake kira (Gazet) wace take
dauke da irin canje canje, na sabbin tsarin dokokin wannan kungiya, kamar yadda siffar tsarinsa
yake a yanzun, kuma zata dinga fitowa loto, loto.

(A) domin kaddamarwa da ayyanarwar sabbin dokoki da za'a kara su sannan kuma aka
tabbatarda su akan abinda ke cikin tsarin dokokin nan.

wannan shine hoton kundin tsarin mulkin na farko.

3. Babu wani sashi acikin wannan dokokin kungiya tamu, da aka yarda a cire shi a, buga, ko
sake rubuta shi ko rageshi, ko canzashi, in ba da yardar majalisar kolin kungiyaba, ta izalatil
bidi'a.

(ga wani hanzari ba gudu ba, idan kuna biye da mu zaku ga tsakanin kafa committee nan da
kaddamarda kungiyar a township stadium jos, wata daya ne. zaku ga kuma kungiyar tana amsa
jama'atil izalatil bidi'a ne kawai ba wa'ikamatis sunnah, sai bayan kaddamarwa ne take amsa
jama'atu izalatil bidi'a wa'ikatis sunnah, saboda shawarar da mal. abubakar gumi ya aiko mal.
lawal abubakar da shi ranar kaddamarwa. wannan yana karyatar da masu neman karkatar da
tarihi na gaskiya masu cewa an kafa kungiyar ne karkashin kulawar mal. Abubakar gumi da
mal. ismaila idris a matsayin shugaban malamai. fadan wannan magana karkatar da gaskiya ce.
ni a ranar wadanda nasan sun halarci wannan kaddamarwa daga wajen jos baya ga mal. lawal
abubakar da mal.ibrahim arab sai mal. ahmadu mai dan koko)

1. SUNA: Tabbataccen sunan kungiya shine, "jama'atu izalatil bidi'a".

(a) MA'ANARSA: kawarda bidi'a, a addinin islam wanda wasu suka cusa daga baya, domin
batawa, da gurgunta ginshikan nan na islam.

(b) jama'atu izalatil bidi'a, kungiya ce ta musulunci, da aka kagata kuma take da hedkwata a jos,
jihar plateau, kuma izalatil bidi'a, ba DARIKA ce ba, kuma ba kungiyar asiri ba ce, kuma ita bata
amince da duk kage kage, ko kuma karin wani sabon abu ba, da akaiwa wani annabi, wanda
baya cikin sakonda sarki Allah ya aiko manzon sa da shi, kuma baya cikin sahihin hadisan
annabi muhammdu, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

(c) IZALATIL BIDI'A, kungiya ce ta addini tsantsa wadda bata dogara ba da komai sai
"ALKUR'ANI DA SAHIHAN HADISAI", kuma ba ruwanta da sha'anin "SIYASA", ko nuna
"banbancin iri", (launin fata" ko KABILANCI, ko kuma jinsin mutane.

(h) IZALATIL BIDI'A, ta dogara ne kawai da ALKUR'ANI da kuma hadisan annabi muhammad
(S.A.W).

JARIDAR AMINIYA ta ranar juma'a 15 zuwa 21 ga afrilu 2016, 7 ga rajab 1437 bayan hijira.
shafi na 27. wani da ya kira kanshi Daraktan watsa labarai na izala alhaji Ali Dan Abba yana ma
fadilatu sheikh sani yahaya raddi akan maganganu daban daban.
yace " Abu na biyu malam yace sheikh ismaila idris shi ya kafa wannan kungiya, mu kuma
muna cewa a'a domin kundin tsarin mulkin kungiyar ya gwada cewa ba mutum daya ne ya kafa
kungiyar ba. ko a yau idan aka dauko kundi za'a ga sa hannun malamanmu kamar sheikh
yakubu musa hassan katsina wanda shi ne shugaban kwamitin da'awa a bangarenmu, yana
daga cikin amintattun kungiya da suka sanya hannun. sannan akwai dokta alhassan sa'id adam
jos wanda shine daraktan kula da makarantun kungiyar na kasa, yana daga cikin amintattu. shi
malam da ke wancan bayanai, ba sunansa a ciki, don haka ba wani gorin da za'a yi mana".

kafin ince komai akan wannan magana taka.

1. alh. Ali lokacin da ake kafa kungiyar kana ina?

Alhaji Ali Abba mal. sani yahaya yace mal. ismaila idris ne ya kafa kungiya kace kun ce a'a, to
ni na karfafa mal. sani yahaya nace mal. ismaila ne ya kafa kungiyar jama'atu izalatil bidi'a, ka ji
abinda kundin tsarin mulkin kungiyar yace, wannan kungiya tayi babban taro a Jos, wanda ina
daya daga cikin mahalarta taron ,a babban birnin jigon wannan kungiya wanda wannan taro
kuwa wanda tayi ranar 14/3/1981 saboda gyare gyare da zatayi na ka'idoji da dokokin ita
wannan kungiyar, daga wannan zama ne har takai ga an nada wakilai na munatane 14 don
wannan gyara, wadannan wakilai kuwa da aka nada (malamai 7) (masu sanin harkokin zamani
7). mu da muka nada wakilan mun tabbatar mal. ismaila ne kafa kungiyar, basa hanun kowa
acikin wannan tsarin mulkin, ba kamar yadda kace akawai sa hanun mal. yakubu musa da Dr.
alhassan sa'id. Kuma ni nasan dalilin rashin sa hanun kowa akan littafin. mal. yakubu musu da
mal. alhassan ma sun san dalili wani abu ne da sai dangida.

Alh Ali Dan Abba Naga Ranka Yabaci Don Malam Sani Yahaya Jingir Yace Muku Yara Dan
Abba Idan Banda Yaratar da Rashin Sanin Tarihin IZALA Mai Zaisa Kace Kundin Tsarin Munkin
IZALA yce Wasu Mutanene Suka kafa IZALA Afahimtarka Da wasu Irinka Ba Malam Ismaila
Idris ne Yakafa IZALA Ba.Wanda Malamanka Bazasu Iya Fadan Hakaba

Kaman Su Mal. Yaqubu Musa Mal. Alasan Saidu Mal. Usman Taliyawa Inzasu Iya Gasgantaka
Cewa Ba Malam Ismaila Idris Ne Yakafa IZALA Ba To Bismilla Muna Sauraron Su.

A Hoton nan kuna iya Ganin Wasu Jamaa Suna Sauraron Mal. Ismaila Idris Yana Waazi Amasu
Sauraron Harda Mal. yahaya Kaduna Vom. Alh. Meriga Yayin Da Mal. Musa Dan Kaho Ke Jawa
Mal. Ismaila Idris Baki.

M. ISMAILA IDRIS. M MUSA D/KAHO. M. YAHAYA K/VOM. ALH. MERIGA Duk Sun Koma Ga
Allah Kamar Yanda Muma Zamu Koma Gareshi.

Allah ya Karbi Kyawawan Aiyukansu Ya Yafe Musu kura kuransu


Alh. Ali Dan Abba in banda yarintarka da rashin sanin kungiyar, kana bugun kirji da kundin
tsarin kungiyar da trustee da register, ina kake aka rubutawa yan sanda da sss na dukkan
jihohin nigeria ranar 1/7/1991 wai anyi taro na masu ruwa da tsakin kungiyar a jos ranar
29/6/1991. An dakatar da mal. ismaila idris da mal. Usman muhammad da Director agaji Alh.
Isa waziri. daga mukamansu, an dakatar da su daga yin wata hulda ko wani aiki kai tsaye ko a
fakaice da sunan wannan kungiya.

sa hannun ALH. MUSA MAI GANDU MUHAMMAD. Duk da wannan takarda hukuma bata taba
dakatar da mal. ismaila ba, daga shugaban wannan kungiya kuma wanda ya kafata koda da
dakika daya, mal. har ya rasu shine shugaban malaman kungiya kuma wanda ya kafata . Bayan
mal. ya rasu mun cigaba da kiranshi wanda ya kafa kungiyar. Muna rubutawa a motocin
kungiya da gine ginenmu da duk wani abu mallakarta, hukuma bata taba rufe mana office ko
makaranta ba.

wannan bakar takarda batayi amfani ba.

Alh. ali dan abba, in banda yarinta da rashin sanin kungiya takardar da aka rubutawa
commissioners na yan sandan jihohi da shugaban sss na jihohi ranar 1/7/1991, wanda take
nuni ga, wai masu ruwa da tsakin kungiyar sunyi taro a jos 29/6/1991 sun sauke mal. ismaila
idris da mal. usman muhammad mataimakin shi da mal. isa waziri, sun ba mal. rabiu daura
shugabancin malamai da mal. Aliyu sani abubakar shugaban yan agaji. Wannan tsabagen
karyace, don idan ka kasa masu ruwa da tsakin kungiyar kashi uku, kashi biyu da rabi acikin su
basu san wannan magana ba, sai dai ace wasu gungun marasa kishin musulunci da ci gaban
shi acikin kungiyar sun taru sunyi abinda ransu ke so. kuma wannan abun da sukayi ya jawo wa
kungiyar ci baya ainun, wanda a lokacin ana fahimtar kungiyar sosai sukayi wannan aika aika.
Dan abba in ba don wasunsu sun rasu ba, da na ambaci wasu da irin abubuwan da suka tayi in
anzo taro, amma duk da haka in halin in ambace su ya kama, zan ambace su.

An kaddamar da kungiyar ranar lahadi 12/3/1978 misalin 8:30am zuwa 1:30pm a jos, to bayan
kaddamarwa sai wa'azi ya budu, maimakon da mal. ismaila idris shi kadai ya ke wa'azi tun daga
8:30am har zuwa 4:00pm. shi kadai ke jan baki yake fassarawa. a kazo aka samu mai jan baki
irin su mal. musa dan kaho, alh. sabo kinzil, mal. alhassan sa'id, mal. umar mika'il da dai sauran
mahaddata. bangaren masu wa'azi akwai irinsu mal. musa muhammad alkali (dan matsaro) da
mal. muhammad musa alkali (dan asabe) da mal. sani yahaya jingir da mal. sa'id hassan jingir
da mal. adam ibrahim da mal. abdullahi mai lafiya da mal. ibrahim salihu (bob malam) da
ibrahim umar da dai sauransu. a cikin manyan maluma wanda tun a lokacin sun manyanta
akwai mal. sa'idu abdullahi (limamin laranto) da mal. yahaya kaduna vom da mal. hamma misau
da mal. abubakar limamin yan taya da sauran su. bangaren masu hali da yan siyasa akwai alh.
shehu muhammad (tobacco) da alh. garba pasali.

Potrebbero piacerti anche