Documenti di Didattica
Documenti di Professioni
Documenti di Cultura
3 things that
make a person:
-Hardwork
-Sincerity
-Commitment
PART 1
Zeenat yarinya ce karama yar shekara 15 tana SS2 iyayenta talakawa ne saidai suna
da rufin asiri suna xaune a unguwar federal lowcost cikin garin bauchi asalinsu
mutanen yola ne aiki ne yakawo mahaifanta garin bauchi Abbu suke kiran
mahaifinsu,mamarsu kuma Ammi qannen zeenat 2 amirah tana Jss3 da amir yana primary
6 daidai gwargwado iyayen suna kula da yaran kuma sun samu ingantacciyar
tarbiyya,kasancewar Abbu da ammi duka sunyi ilimin boko dana islama shiyasa yaran
ma suke da natsuwa qwarai da gaske! Akusa da gidnsu zeenat gidan wani attajiri ne
da ake kira da Alh Ahmed yanada kudi kuma harkar business dinsa yafi yinta a qasar
waje!,Akwai dansa kamal dayake son zeenat kamar ransa!,Har anyi musu baiko a halin
yanzu jira ake ta gama makaranta ayi masu aure,yana da qannai mata da maza ataqaice
dai gidansu babban gida ne,ita dai zeenat baxata iya dorar da komi akan soyayyar ta
da kamal ba abinda dai tasani shine tana matukar ganin girmansa don xamu iya cewa
yarinya ce kusan ma batasan menene so ba. Zeenat tana da matuqar kyau irinnasu na
asali kuma na gado wato fulanin asali fara ce tas tana da kyan qira dirarriya ce
tsabar kyanta dake ruda samari suna tururuwa a qofar gidansu shne yasa kamal ya
daga hanklinsa wajen ganin cewa anyi masu baiko don hanklainsa ya kwanta!. Mafi
yawancin yan layinsu da unguwar sukan kirata da Raani yar indya,natsuwarta da kamun
kanta ne yasa mutane da dama suke son yarinyar hatta da magidantan unguwar sukanji
ina ma ace yarinyar nan yarsu ce? Wasu kuma sukanso ace aurenta sukayi.Tafe take a
gajiye tana dawowa daga makaranta don acikin fomwan suke karatu ta cikin fed lwcst
qannenta sun riga sunkoma gida tun dazu itace sai qarfe 4 don tana tsayawa lesson
kamal ne xaune akan motarsa shida wasu abknsa biyu suma da alamun ya'yan masu kudi
ne ta iso wajensu tadan rusuna ta gaidasu mubarak ya dubeta yace amaryarmu sai
yanzu aka taso? Tayi murmushi tace eh tana qoqarin wucesu don abbu yahanata magana
kan hanya!,kamal ne ya duro daga kan motar yafara taka mata tare dasa hannu ya
karbi skul bag dinta yana cewa ran gimbiya ya dade! Kanta a sunkuye tana murmushi
suka ci gaba da tafiya yana cewa yau kin wahalar dani inata jiran dawowarki don
kawai inga wannan pretty face din! Tunda abbu ya hana ni xuwa dauko ki a
mkrnta......